Jajircewa Da Yin Aiki Tukuru Yana Samar Da Nasara Ga Dan Gwagwarmaya – Golam Rabbzni Nayan

News

Hadin guiwar kungiyoyin yancin dan Adam da kasar Isara’ila Da Indiya sun karrama Golam Rabbani Nayam Bangalee da lambat yabo mafi daraja da nuna yabawan su akan gudunmawar da yake bayarwa ga rayuwar al’umma, yancin dzn Adam, da kudurim shi na samar da zaman lafiya, yada labarai da ilimi.

Taron wanda aka gudanar da shi a Minna ta jihar Nejar, Nijeriya. Shirin mai taken ” Global Celebration Cremony” wato taron murnar farin ciki na duniya, an shirya ne dan karrama Golam Rabbani Nayan Bangalee saboda fahimtar irin gudunmawar da yake bayarwa a siyasar duniya, wanda ya gabatar da wasu tsare-tsaren shugabanci na duniya da kirkiro tsarin siyasa zamani wadda za tayi aiki ba tare da shiga hakkin kowa ba. ( Tsarin Zamantakewa)

Kumgiyoyin da suka bada lambar yabon ta ilimi sune:

Leeway Peace and Human Rights Foundation,

Notable Book of World Records Nigeria,

Lectern Peace and Human Rights Academy Nigeria,

Unison Dialogue Global Chain Nigeria,

Alliance of the Peoples of the World Israel/Russia,

World Human Rights and Peace Commission India.

An karrama Golam Rabbani da lambar yabo ta Global Educator, lambar yabo ta ilimi ta duniya, da Global Peace, lambar Yabo ta zaman lafiya na duniya, Leadership Award, da lambar yabo ta shugabanci, sai lambar yabo ta Humanitarian Ambassador, jakadan jinkai, Peace Advocate wato jagoran zaman lafiya, kuma Goodwill Ambassador, wato jakadan nuna kauna ga jama’a kuma Most Distinguished Media Person in the World. Sannan fitaccen dan jarida a duniya.

Farfesa Buhari Isah ne ya jagoranci gabatar da lambobin yabon.

Daga Awwal Umar Kontagora.

share
Share on facebook
Facebook
Share on twitter
Twitter
Share on linkedin
LinkedIn
Share on pinterest
Pinterest
Share on telegram
Telegram